Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Yawan Haihuwa Da Auren Mata Rututu Na ‘Yan Arewa Ne, Ke Haifar Da Matsala A Mulkin Tinubu – Fayose

FB IMG 1722402837249

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya soki lamirin jama’ar Arewa na yawan aure da haihuwar ‘ya’ya ba bisa ka’ida ba, a matsayin babban dalilin da ke haifar da matsala a mulkin Shugaba Tinubu.

An ruwaito Fayose na wannan furuci ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, inda ya koka da yadda ‘yan arewa ke mayar da hannun agogo baya wajen ciyar da Najeriya gaba.

” Na yi hira da wasu ƴan Arewa a lokacin da na ziyarci yankin, sai kaji mutum yana karbar albashin Naira dubu 40 amma yana da ƴaƴa 16 da Mata hudu, haka dai zaka ji sun tara mata da yara barkatai, kuma babu wani tsari da suka yi”

Sai dai da yawa daga cikin jama’a musamman ‘yan Arewa ba su ji dadin kalaman na Fayose ba, inda suka bayyana shi a matsayin cin mutunci ga jama’ar Arewa tare da yin kiran ya yi gaggawar neman afuwa ga jama’ar Arewa.

Exit mobile version