Yawan Haihuwa Barkatai A Najeriya Ne Silar Matsalar Tsaro A Kasar – Obasanjo

Rahotanni daga Abeakuta babban birnin Jihar Ogun na bayyana cewar Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilan aikata laifuka a Najeriya. A cewarsa, ta’addanci, fashi da makami na karuwa a Najeriya sakamakon karuwar yawan mutanen kasar.

A zahirin gaskiya, tsohon shugaban kasar ya ce wannan yana hana shi barci cikin dare, yace yawan matasa marasa aikin yi ne matsalar Najeriya da haihuwa barkatai.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin gabatar da rahoton kungiyar cigaban Afirka ta 2020 (APG) a Legas mai taken: ” Making Africa’s Population an Asset”, a ?arshen mako.

Tsohon shugaban ya dage cewa dalilin tayar da kayar baya da ta’addanci a kasar bai yi nisa da kasancewar akwai tarin matasa marasa aikin yi da ake daukar su cikin kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da kungiyoyin masu aikata laifuka ba.

“An ce Mohammed Yusuf wanda ya fara Boko Haram mutum ne mai nagarta da sanin yakamata tare da dimbin matasa marasa aikin yi da ke jira domin su saurare shi. Na ji akwai lokacin da ya kira mabiyansa ya ce wa daya, ‘ka je jami’a, shekaru nawa yanzu da ka kammala?’

Ya ce shekara uku kuma me kake yi yanzu? Ya ce, ‘babu aiki.’ Sannan ya amsa, ‘ka ga rashin amfanin ilimin jami’ar ka.” “Ta haka ne kalmar Boko Haram ta bullo.

Ta hanyar mabiyansa ba su da ayyukan yi, ya ce ‘kun ga rashin amfanin ilimin ku na boko.’ Idan ba za mu iya samar da ayyukan yi ga yawan mutanen mu ba, da gaske muna cikin matsala. Babu bukatar wani ya gaya mana wani abu.”

Related posts

Leave a Comment