Yawan ?abilu Da Addinai Ne Silar Matsalolin Najeriya – Osinbajo

An bayyana cewar yawan tarin ?abilu da addinai barkatai da Najeriya ke fama dasu, sune manyan matsaloli da suka yi wa Najeriya tarnaki suka hanata motsawa, ballantana har ta kai ga matsayin gogaiya da sauran ?asashen duniya.

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan lokacin da yake tsokaci dangane da halin koma baya da tarbarberawar al’amura da Najeriya ke fama da su.

Wata sanarwa daga Laolu Akande, mai magana da yawun Osinbajo, ta nakalto shi yana cewa aikin gina kasar na iya zama kalubale duba da yawan kalubalantar juna ta fuskar dabi’u da hakurin ‘yan kasa daga sassa daban-daban.

Ya yi wannan magana ne a wani taro kan ci gaban kasa da jaridar Global Patriot tare da hadin gwiwar karamin ofishin jakadancin Najeriya da ke New York da kuma kungiyar ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDO), reshen New Jersey suka shirya.

Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa gina kasa “kalubale ne da aka jefa shi ga kowa, ya yi gini, ba ya rusa ba” kuma “a tara, ba a kwashe ba.” “Aikin gina kasa yana aiki kuma har ma yana iya zama kamar rikici yayin da ake ci gaba, musamman a cikin kasa mai kabilu da addinai daban-daban kamar Najeriya,”

Dole ne mu yarda da cewa akwai bukatar kara rarraba karfin ‘yan sanda. Na kasance mai yawan bayar da fatawa kan harkokin ‘yan sanda na jihohi kuma na yi imanin haka lallai na iya zama dole kuma hanyar da za mu bi,”

“Majalisar Dokoki ta Kasa na cikin wani matsayi na yin la’akari da wasu shawarwarin da suka je musu da nufin mika karin iko ga jihohi don ingantawa da kuma magance matsalolin tsaro.”

Related posts

Leave a Comment