Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a Najeriya.
Hakan ya tabbatar da cewa yau Litinin za ta kasance 1 ga watan Ramadan, wato ranar da al’ummar Musulmi a duka sassan ƙasar za su tashi da azumin wannan shekara.
Ƙasashe da dama sun sanar da ganin watan na azumi a jiya Lahadi, ciki har da Saudiyya.
Ya yi kira da a yi wa ƙasa addu’a, musamman a daidai wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa da kuma matsalolin tsaro.