Yau Litinin Jama’ar Musulmi A Najeriya Suka Tashi Da Azumin Watan Ramadan

IMG 20240310 WA0411
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a Najeriya.

Hakan ya tabbatar da cewa yau Litinin za ta kasance 1 ga watan Ramadan, wato ranar da al’ummar Musulmi a duka sassan ƙasar za su tashi da azumin wannan shekara.

Ƙasashe da dama sun sanar da ganin watan na azumi a jiya Lahadi, ciki har da Saudiyya.

Ya yi kira da a yi wa ƙasa addu’a, musamman a daidai wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa da kuma matsalolin tsaro.

Labarai Makamanta

Leave a Reply