Yariman Saudiyya Ne Ya Bada Umarnin Kashe Khashoggi – Amurka

Jamal Khashoggi

Wani rahoto da Amurka ta saki kan bayanan sirrin da ta tattara kan kisan ?an jaridar nan na Saudiyya Jamal Khashoggi, ya nuna cewa Yariman ?asar mai jiran gado Mohammed bin Salman ya amince da wani shiri na kashe ?an jaridar.

An kashe Mista Khashoggi a 2018 a ofishin jakandancin Saudiyya a birnin Santambul.

Rahoton ya ce Yariman na ?aukar Mista Khashoggi a matsayin barazana, inda ya goyi bayan a ?auki ko da mummunan mataki ne domin rufe bakinsa.

Mista Biden na bu?atar masu kare ha??in bil adama da su taka muhimmiyar rawa a dangantakar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya, kuma ?aya daga cikin rawar ita ce fallasa wannan rahoton sirrin.

Tun bayan kisan da aka yi wa Khashoggi a ofishin Jakandancin Saudiyya dake kasar Turkiyya, jama’a da dama ke cigaba da bayyana ra’ayoyin su akan kisan, inda mafi yawa suka zargi Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman.

Abin da ya saura yanzu dai shine jiran martanin da kasar ta Saudiyya za ta mayar akan zargin da Amurkan ta yi mata, kasancewar ta Babbar kawa a wajen ta.

Related posts

Leave a Comment