‘Yar Majalisa Na Neman A Halatta Noman Wiwi A Najeriya

Honarabul Princess Miriam Onuoha mai wakiltar yankin Okigwe ta Arewa daga jihar Imo ce ta kai wannan kudiri majalisar.
A halin yanzu wannan kudiri da Hon. Miriam Onuoha ta gabatar, ya kai matakin sauraro na biyu.

Wani masanin harkar shari’a, Dr. Tonye Jaja Clinton ya bayyana wannan a wajen wani taro da kungiyar Grow Cann Africa ta shirya da ‘yan jarida.

Da ya ke magana a garin Abuja, Tonye Jaja Clinton ya bayyana irin amfanin noma ganyen wiwi da kuma fa’idar mansa da ake amfani da shi, Cannabidiol.

Grow CANN Africa ta na kokarin ganin Najeriya ta yi amfani da baiwar da Ubangiji ya yi mata na wiwi, wanda zai iya jawo mata Dala biliyan 10 a 2020.

Shugabar wannan kungiya, Uju Adaku, ta yi bayanin yadda za a iya samun riba idan aka ba mutanen kasar waje damar noman wiwi da kuma aiki da shi.

A dalilin haka ne wannan kungiya ta zauna da Jakadun kasashen Kanada da ke Najeriya da hukumomi irinsu NAFDAC, NDLEA da ma’aikatar noma.

Adaku ta ce Grow CANN Africa ta na neman a rika cin moriyar wiwi a Najeriya ta hanyar kwarai. Doka ta haramta aiki da wiwi saboda bugar wa da ya ke yi.

Jaja ya bayyana cewa idan wannan kudiri ya samu karbuwa a majalisar wakilai, zai je gaban Sanatoci, daga nan kuma a mika sa zuwa teburin shugaban kasa.

A makon jiya kun ji cewa Jami’an hukumar NDLEA da ke yaki da fataucin kwayoyi, sun gano wata babbar gonar tabar wiwi a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya.

Dakarun NDLEA sun lalata wannan gonar tabar wiwi wanda darajarta ya kai akalla N1.2bn.

Labarai Makamanta

Leave a Reply