Ƙungiyar Dattawan Arewa ACF ta bayyana cewar yankin Arewacin Nijeriya na cikin wani babban ƙalubale na fuskantar barazanar tarwatsewa muddin shugabanni da jama’ar yankin ba su farka daga barcin da suke ciki ba.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar bayan kammala taron ta a kaduna, wadda ta samu sanya hannun shugaban kungiyar tuntuba ta magabatan na Arewa Mista Audu Ogbeh kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.
Sanarwar ta bayyana cewar wasu jama’a na kuskuren fahimtar manufar kungiyar Dattawan Arewa ta ACF, inda wasu ke danganta kungiyar da ta addini ko ƙabilanci ko kuma ta siyasa, a magana ta gaskiya babu ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da kungiyar ta doru akai, yankin Arewa yanki ne da ke da ƙabilu sama da 300 masu bin addinai daban-daban, saboda haka babu gaskiya akan zargin.
Yankin Arewa a yanzu na fuskantar barazanar da a baya bai fuskanta ba, duba da yadda harkar tsaro ke kara taɓarbarewa, kisan jama’a dare da rana, ashe lokaci ya yi da zamu miƙe gaba ɗaya domin fuskantar wannan babban ƙalubale.
Ƙungiyar ta Arewa ta yi kira da babban murya ga gwamnonn jihohin Arewa 19 da babban birnin tarayya Abuja da cewa, su tabbata cewa jama’ar yankin sun ci gajiyar bashin Naira biliyan 75 da gwamnatin tarayya ta fitar domin amfanar manoma a fadin Najeriya.
Sannan Dattawan sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da sauran gwamnatocin jihohi da su tashi su fuskanci matsalar da yankin Arewa ke fuskanta na talauci da zubar jini a kullum.
Ya zama wajibi gwamnatocin Arewa su mayar da hankali wajen inganta bangaren noma a yankin, duba da ganin irin tasirin da bangaren ya ke dashi wajen ciyar da ƙasa gaba.
Ɓangaren Ilimi da ayyukan yi sun zama wata matsala da ke addabar yankin Arewa, saboda haka Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci gwamnatocin Arewa da yin dukkanin mai yiwuwa wajen shawo kan matsalar.