Wasu gungun batagarin Matasa cikin ayarin masu Zanga-zangar SARS sun balle wani gidan yari da ke kan hanyar Sapele a birnin Benin na jihar Edo da karfin tuwo bayan sun fatattaki jami’an da ke kula da gidan Yarin.
Matasan sun saki dukkanin masu laifin da ke tsare a gidan Yarin, inda suka fantsama cikin gari, lamarin da ya firgita jama’a mazauna babban birnin jihar.
Ɓalle gidan yarin na zuwa ne a daidai lokacin da zanga-zangar neman rushe SARS ke kara zafi a Benin da sauran jihohin kudancin Najeriya.
Duk da babu cikakken rahoto daga kafafen yada labarai, sannan babu sanarwa daga hukumar kula da gidajen yari ta kasa, faifan bidiyon yadda batagarin su ka kai hari gidan yari ya shiga yanar gizo.