Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewa kungiyar ISWAP ta kammala dukkan shirye-shirye domin bude sabon gidan rediyo na musamman. Kungiyar ta shirya bude gidan rediyon ne a yanar gizo mai suna “Radio Raeed” domin yaɗa manufofinta. ‘Yan ta’addan ISWAP za su samar da gidan rediyo domin wayar da kan Mutane.
ISWAP ta ce za ta yi amfani da gidan rediyon domin shawo kan jama’a shiga kungiyar musamman a yankin Arewa maso Gabas.
An ruwaito cewa gidan rediyon zai kasance a Kangarwa wanda zai ba da karfi wurin kafa shari’ar Musulunci a yankin. Har ila yaushe, za a rinka gabatar da shirye-shirye a cikin harsunan Hausa da Larabci da kuma Kanuri.
Wannan mataki na kungiyar ya kara tabbatar da yadda suke samun ƙarfi musamman a Arewa maso Gabas, cewar rahoton.