Jarumin finafinan Kudun ya ce tun kafin fim din ya fita kasuwa har ya fara samun sakonnin barazanar kisa ta hanyar kafofin sadarwa ta zamani. Wanda ya bayyana hakan a matsayin babbar barazana ga rayuwarsa.
Peter Edochie ya kara da cewar ‘ya’yan kungiyar Shi’a ne ke aiko da masa da barazanar kisa, sakamakon fitowa da ya yi a matsayin jagoransu Zakzaky, wanda kowa ya sani cewa wasan kwaikwayo ne ya yi.
“Ina amfani da wannan dama in sanar da jami’an tsaro da iyalina da sauran jama’a baki ɗaya cewar rayuwata tana cikin hatsari daga hannun ‘yan Shi’a, tun bayan fitowa a shirin Fim na “Fatal Arrogance” da na yi a matsayin Zakzaky, idan kun ji labarin mutuwata to ‘yan Shi’a ne”
A gefe guda kuma jarumin Finafinan Hausa Yakubu Muhammad ya bayyana ficewar shi daga cikin fim din, sakamakon yadda ya ke ta samun kiraye kiraye da barazana daga wasu, sannan ya tabbatar da cewar ya mayar da dukkanin abin da ya karba daga masu shirya fim din.
“Kafin a kawo mini tallar shiga fim din ko kaɗan ban da labarin cewa a wallafa wani littafi mai suna “Fatal Arrogance” dake alakanta ‘yan Shi’a a matsayin ‘yan ta’adda, wannan shine dalilin shiga ta ciki tun farko”
Tuni dai ‘yan Shi’a suka rubuta takardar koke ga shugaban ‘yan sanda, inda suke tuhumar rundunar soji da ɗaukar nauyin shirin Fim ne, tare da kiran a dakatar da shirin Fim din nan take.