‘Yan Sanda Sun Nesanta Kansu Da Kama Matashin Da Ya Soki Aisha Buhari

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa, tace ba ta da hannu wajen cafke wani dalibi mai suna Aminu Muhammad da ake zargin tayi. Ana zargin Aminu Muhammad yana hannun dakarun ‘yan sanda bisa zargin da ake yi masa na cin mutuncin uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari.

Da aka tuntubi ‘yan sandan jihar Jigawa, sun tabbatar da cewa Aminu Muhammad bai hannunsu, kuma ba su iya yin wani bayanin inda ya shiga ba. Kakakin rundunar jihar, DSP Lawan Shiisu ya shaidawa manema labarai cewa bai da labarin jami’an sanda sun dauke wannan dalibin jami’ar FUD a garin Dutse.

“Ba mu cafke shi ba. Ba zai yiwu a cafke mutum a yankina ba tare da an sanar da ni ba.”

Ana zargin matashin yana hannun jami’an hukumar DSS. A wani kaulin, hukumar DSS ta cafke Aminu, ta wuce da shi zuwa birnin Abuja, inda aka rika yi masa dukan tsiya a gaban uwargidar shugaban Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply