‘Yan Sanda Na Iya Shawo Kan Matsalar Tsaro – Tsohon Shugaban ‘Yan Sanda

Tsohon Shugaban rundunar ‘yan sandan ?asar nan, Ibrahim Kpotun Idris, yayi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya ta ?auki sabbin jami’an ‘yan sanda matu?ar tana son ta kawo ?arshen ?alubalen tsaron da ya?i ci ya?i cinyewa a ?asar musanman yankin Arewacin ?asar.

Idris yace dalilin da yasa matsalar tsaro take cigaba da ruruwa a ?asar nan shine saboda rashin isassun jami’an yan sanda da kuma rashin kula da su yadda yakamata.

Tsohon Sufetan wanda ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, yace idan ka kwatanta adadin ‘yan sanda da yawan al’ummar Najeriya, zaka tabbatar da babu isassun jami’an yan sanda a Najeriya.

“Babbar matsalar itace babu isassun ‘yan sanda, jami’an na aiki ne a wahalce idan ka ha?a da yawan al’ummar da muke dashi a Najeriya. “Na wani ?an lokaci, inda gwamnati zata ?ara yawan ‘yan sanda domin da?ile matsalar tsaro, to hakan zai taimaka sosai.”

“Haka kuma, yakamata gwamnati ta gyara bu?atun ‘yan sanda, ta ?angaren walwala da jin da?insu da sauran bukatunsu. Matu?ar gwamnati tayi haka to tabbas ?asar nan zata dawo yadda aka santa.”

“Akwai abubuwa da yawa da yakamata ayi domin ?ara ma jami’an ‘yan sanda ?arfi, su kuma su sami damar da?ile duk wasu laifuffuka a ?asar nan.” a cewarsa.

Idris ya nuna rashin amincewar sa da shirin ?ir?iro sabbin jami’an yan sandan jihohi, Yace ?irkirar wa?ansu jami’ai daban kuma bayan wa?anda ake dasu zai sa tsaro ya ?ara ta?ar?arewa ne kawai.

“Maganar jami’an tsaron yankuna, bana tunanin shine hanya mafita, ina ganin sai-dai su rage ma jami’an ‘yan sandan mu karfin gwuiwa, ina ganin ya kamata gwamnati ta dakatar da wannan shirin cikin gaggawa.”

Related posts

Leave a Comment