Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sifeta janar na ?an sanda Usman Alkali Baba ya bayyana cewa rundunar ?an sanda ?asar ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan zargin kai hari a kan jerin gwanon motocin ?an takarar shugaban ?asa na jamiyyar PDP Atiku Abubakar.
Lokacin da yake bayani a taron ganawa da ?an jarida na ministocin ?asar a ranar Alhamis, Alkali ya ce yana iya yiwuwa mai magana da yawun rundunar a jihar Borno ya yi hanzari a bayaninsa game da harin.
Ya ?ara da cewa za a duba irin bayanan da suka fito daga ?angarori daban-daban domin tantance gaskiyar lamarin.
A ranar Laraba ne jamiyyar PDP ta yi zargin cewa an kai wa jerin-gwanon motocin ?an takarar shugaban ?asa na jamiyyar a Maiduguri, wani abu da rundunar ?an sandan ta musanta.