Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sifeta janar na ƴan sanda Usman Alkali Baba ya bayyana cewa rundunar ƴan sanda ƙasar ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan zargin kai hari a kan jerin gwanon motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Lokacin da yake bayani a taron ganawa da ƴan jarida na ministocin ƙasar a ranar Alhamis, Alkali ya ce yana iya yiwuwa mai magana da yawun rundunar a jihar Borno ya yi hanzari a bayaninsa game da harin.
Ya ƙara da cewa za a duba irin bayanan da suka fito daga ɓangarori daban-daban domin tantance gaskiyar lamarin.
A ranar Laraba ne jam’iyyar PDP ta yi zargin cewa an kai wa jerin-gwanon motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a Maiduguri, wani abu da rundunar ƴan sandan ta musanta.