‘Yan Najeriya Za Su Yi Nadamar Rashin Zaman Mahaifina Minista – Bello El-Rufa’i

IMG 20240310 WA0412

Dan Majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai ya ce Najeriya ta rasa jigo bayan majalisa ta ki amincewa da mahaifinsa. El-rufai ya ce kin amincewa da Majalisar ta yi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai babbar asara ce ga kasar.

Bello ya bayyana haka ne yayin hira da dan jarida Seun Okinbaloye da Punch ta ruwaito inda ya ce mahaifin nasa tun farko ba ya son mukamin.

Ya ce sai da suka hadu da shi da sauran iyalansu domin rokon tsohon gwamnan ya karbi mukamin minista a gwamnatin Bola Tinubu. Ya kara da cewa ya ji takaici sosai bayan kin amincewa da mahaifinsa a Majalisar inda ya ce tabbas an tafka babban rashi a wannan gwamnati.

“Ina cikin Majalisar lokacin da aka ki amincewa da mahaifina, na ji takaici a lokacin kuma har yanzu ina jin zafin haka.” “Da ni da gwamnan Kaduna, Uba Sani da wani kwamishina a lokacin mulkin mahaifina mun taka rawa sosai wurin rokonsa domin ya karbi mukamin.”

“Tun farko shi ba ya bukatar mukamin, amma zai yi wahala ‘yan Najeriya su yarda da haka saboda sun yi tsammani kowa ya na son mukamin Minista.”

Bello ya ce tabbas ba ya son mukamin mune muka matsa masa amma kuwa da ya karba za a samu sauyi a wannan gwamnati matuka.

“Shugaba Tinubu ya na son yin aiki tare da shi domin har Kaduna ya zo kan lamarin, mun yi tunanin zai ba shi ma’aikatar makamashi ko kuma iskar gas.” “Mutane da yawa basu san mahaifina ba, mutum ne mai saukin kai amma ana yi masa mummunan fahimta.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply