Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki APC Bola Tinubu, a ranar Talata ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa kokarin da ya yiwa al’ummar Najeriya na ceto su daga halin tsaka mai wuya da suka tsinci kansu a ciki.
Bola Tinubu ya ce Buhari ya kwantar da hankalinsa kamar tsumma a randa da sannu yan Najeriya zasu fahimci darajarsa bayan ya ajiye mulki.
Dan takaran yace ya kamata ‘yan Najeriya su fahimci cewa Buhari ya tarar da matsalar tsaro da rashawa lokacin da ya karbi mulki daga wajen Jonathan da sauran tarin matsaloli wa?anda ba za su lissafu ba.
“A yanzu ba za’a yabawa kokari da wahalar da Buhari ya sha ba. Amma da sannu za’a fahimci irin namijin gudunmuwar da ya bada.” “Gwamnatin nan ta gaji matsaloli da dama. Daga baya Buhari fuskanci matsalolin da ba’a tsamanni kuma suka sake rikirkita lamura”.