Kungiyar Kwadago da kuma sauran al’umma a Najeriya musamman a kafafen sada zumunci na zamani sun bayyana matukar damuwa da mamakinsu dangane da yadda mahukuntan kasar suka yanke shawarar kara farashin wutar lantarki da kuma na man fetur a lokaci daya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da bayyana damuwa dangane da yanayin fatara da suka tsinci kansu a fadin kasar na matsin tattalin arziki.
Ko a jiya jaridar muryar yanci ta kawo maku ruhoton babban labarin ta inda shugaban kasa Muhammadu Buhari Ke kara ba yan kasa hakuri akan matsin tsadar rayuwa da ake ciki, inda shugaban ya bayyana cewa komai zai daidaita da ikon Allah.