‘Yan Najeriya Shaidu Ne Akan Kokarina Na Samar Da Tsaro – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ‘yan Najeriya sun san gwamnatinsa ta yi iyakan kokarinta wajen shawo kan matsalan tsaro da ake fama da shi a fadin tarayya.

Yayinda yake magana da manema labaran fadar shugaban kasa bayan Sallar Idi a fadar shugaban kasa Aso Villa, shugaban kasan yace ba lokacinsa aka fara fuskantar matsalar tsaro ba.

Amma ya nuna bacin ransa kan gazawan hukumomin tsaro , inda yace ya kamata a ce sun fi hakan kokari.
“Ina son yan Najeriya su farga kan kasarsu kuma su san abinda muka gada lokacin da muka dau mulki a 2015 Boko Haram ne a Arewa maso gabas sannan barandanci a Kudu maso kudu….
‘Yan Najeriya sun san munyi iyakan kokarinmu”

“Abinda ke faruwa a Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya na da matukar takaici amma nayi imanin cewa Sojoji, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su kara kokari.”

A jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki, ya ce Buhari ya tabbatarwa hukumomin tsaro cewa zai kara musu dukiya domin kawar da matsalar tsaron kasar nan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply