Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, za ta sake gudanar da tsare-tsaren kudade a Nijeriya.
Jaridar Leadership ta bayar da rahoton cewa, a wajan kaddamar da taron karawa juna sani wanda ya gudana a birnin Abuja, ministar kudi Hajiya Zainab Ahmed, ta bayyana cewa, harkar sha’anin tsarin kudade na daya daga cikin abubuwa muhimmai da suke jan ragamar harkokin kasuwanci.
Ta kara da cewa, wannan tsarin yana bukatar zuba jari domin kara wa ‘yan kasuwa gwarin giwa wajen bunkasa tattalin arziki da kuma inganta harkokin kasuwanci a ciki Najeriya.
Hajiya Zainab ta ce, wannan yunkuri yana da matukar mahimmanci ga masu ruwa da tsaki su shiga cikin sha’anin tsarin kudade a Nijeriya, inda ta ce tsarin sha’anin kudade ya kwashe tsawan shekarar 10 ba tare da an sake bibiyar aiwatar da wannan fannin ba, wanda yake babban muhimamnci a bangaren tsarin masu zuba jari da ilimi da masana’antu masu sarrafa kayayyaki.
Ta ce a duk lokacin da aka samu nasarar kammala wannan tsarin, za a samu kundi da za su bai wa Najeriya damar cimma burinta na bunkasa sha’anin kasuwanci da hadahadar kudade, kuma zai kara karfafa Najeriya da kudinta a cikin Afirka.