Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, ya jagoranci wani taro na yanar gizo inda ya kaddamar da shirin fadar shugaban kasa na bunkasa hakar gwal (PAGMDI).
Rahotanni sun bayyana cewa, shirin PAGMDI, zai samawa ‘yan Nijeriya akalla 250,000 ayyuka, yayin da gwamnatin tarayya za ta rinka samun kudaden shiga $500m a kowacce shekara.
A cewar wata sanarwa daga Femi Adesina, mai tallafawa shugaban kasa ta fuskar watsa labarai, shirin zai taimaka wajen kawo karshen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma baiwa Nigeria kwarin guiwar samun makoma mai kyau a nan gaba.