A ranar Alhamis ne majalisar dattawan Najeriya ta dage zamanta har zuwa ranar 15 ga watan Satumba domin bai wa mambobinta damar samun hutunsu na shekara-shekara da aka saba a al’ada.
Shugaban majalisar dattawan Sanata Ahmad Lawan, shine ya sanar da hakan bayan wani zaman shugabannin majalisar da aka gudanar a birnin Abuja.
Sai dai Sanata Lawan ya ce ba tare da hanzari ba, kwamitoci daban-daban da za su ci gaba tattaunawa kan wasu muhimman ayyuka da ke bukatar kulawa ta gaggawa, za su ci gaba gudanar da zama yayin da bukata ta taso.
Ya umarci kwamitin majalisar da aka ratayawa hakkokin kula da kudi, da ya hada hannu-da-hannu da Ministar Kudi, Kasafi da tsare-tsaren ci gaban kasa, Zainab Ahmed, domin shirya kudirin kasafin kudin kasar na badi.