‘Yan Majalisa Basu Da Hurumin Tilasta Buhari Gurfana Gaban Majalisa – Malami

Babban ministan shari’a Abubakar Malami SAN ya bayyana cewa majalisa bata da hurumin tilastawa shugaba Buhari gurfana gaban majalisa. Hakan na zuwa ne kasa da awanni 24 da aka tsara cewar shugaban zai bayyana a gaban majalisar a gobe alhamis domin amsa wasu muhimman tanbayoyi akan matsalolin tsaro.

Ko a farkon satin nan mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyanawa manema labarai cewar shugaba Buhari ya amince zai amsa gayyatar da yan majalisar su kai masa kamar yadda shima kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya shaidawa yan jaridu a makon da ya gabata.

Ana ganin janye gayyatar da shugaba Buhari yayi bai rasa nasaba da ganawar da yayi da gwamnonin kasar nan a jiya talata inda suka shawarci shugaban da karya amsa gayyatar kamar yadda wasu majiya suka bayyana.

Anan ganin wannan jawabi na ministan shari’a ya kara tabbatar da kokwanton da ake yi na halartar shugaba Buhari majalisar a gobe alhamis. Malami ya bayyana cewa babu inda kundin tsarin mulkin kasar nan ya ba yan majalisar damar tilastawa shugaba bayyana a gaban su.

Za mu gani ko shugaba Buhari Zai yi amai ya lashe a goben ko kuwa zai kara tabbatarwa duniya shi shugaba ne mai bin doka sau da kafa.

Kuna ganin ya dace shugaba Buhari ya gurfana gaban majalisa domin ansa tanbayoyi kan matsalolin tsaron kasar nan?

Labarai Makamanta

Leave a Reply