Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

‘Yan Kudu Ba Sa Tada Fitina Sai Dan Arewa Na Mulki – Sheikh Lau

An bayyana cewar tsagerun yankin Kudancin Najeriya ba sa tada hankali da kunna wutar fitinar a raba ƙasa sai ya zamana cewar ɗan Arewa ne ke kan shugabancin kasa.

Shugaban kungiyar Izala na ƙasa baki daya Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da aka yi dashi a ofishin Ƙungiyar dake birnin tarayya Abuja.

Sheikh Lau ya kara da cewar a duk lokacin da aka wayi gari ɗan Arewa musulmi na shugabancin kasa zaka tarar da jama’ar Kudu musanman yankin Inyamurai suna ta zuzuta wutar fitina da kaddamar da farmaki akan jama’ar Arewa da sunan batun wai a raba ƙasa.

“Shin ‘Yan arewa ne suka hana raba ƙasar, ko kuwa sai idan an kashe sune zai sanya a raba kasa? Wannan zalunci ne wanda ba za’a a yarda da shi ba”.

Shugaban Izalar ya cigaba da cewar akwai hanyoyi da dama da ake bi idan har batun raba kasa ya taso ba tare da kisa ko cin zarafin wasu ba, akwai majalisar kasa a Najeriya wanda duk wani mutum ke da wakili a ciki, me yasa ba za’a bi ta hanyar tattaunawa ba sai ta hanyar cin fuskar ‘yany Arewa.

Shehin malamin ya tabbatar da cewar Allah ya albarkaci yankin Arewa da arziki tun azal, an san yankin ne ya tsayu wajen gina Najeriya, kuma a yanzu an abin da ake tutiya dashi na arzikin mai yankinr arewa na dashi a Jihohin Bauchi da Gombe, saboda ya kamata a gane ‘yan Arewa ba ci ma zaune bane.

Exit mobile version