Wasu ‘yan kishin al’ummar yankin Lere dake Jihar Kaduna sun baiwa Kakakin Majalisar tarayya Femi Gbajabiamila wa’adin kwanaki sha hudu da zummar ya amince da sauya musu dan majalisar tarayya dake wakiltar al’ummar yankin Lawal Muhammad Rabiu da Injiniya Suleiman Aliyu wanda yake halataccen zababben dan takarar yankin Lere a majaliasar.
Wakilan al’ummar yankin sun bayyana hakan ne a taron yan Jaridun da suka gudanar a Cibiyar Kungiyar Yan Jaridu reshen Jihar Kaduna a ranar litinin inda suka bayyana fushin su bisa kin yin biyayya da Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya yi ga umarnin kotun.
Lauya Suleiman Lere wanda ya jagoranci tawagar, ya bayyana cewa a ranar Juma’ar da ta gaba ne suka mika sakon wa’adin kwanaki sha hudun ga Kakakin majalisar biyo bayan kin amincewa da yin biyayya ga umarnin kotu da ya yi na ci gaba da ajiyar dan majalisar na Jam’iyyar PDP da ba shi ne zababben Dan takarar yankin ba.
Barista Lere, ya kara da cewa dan majalisar dake zauna a kan Kujerar a yanzu, ba shi bane wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya yi nasarar kuma ta bashi takardar shaidar cin zabe ba, amma kakakin majalisar ya ki amince da rantsar da ainihin zababben wakilin yankin Suleiman Aliyu Lere na Jam’iyyar APC.
Ya ce “a don haka idan Shugaban majalisar bai yi abin da ya kamata ba nan da kwanakin da muka ba shi, toh zamuje mu mamaye majalisar har sai an biya mana bukatun mu, saboda wannan zagon kasa ne ake wa kasa da karfin iko domin wannan ba matsalar al’ummar yankin Lere ne kawai ba.”
Acewarsa, dukda yake kotu tarayyar ta dakatar da zababben dan majalisar da farko, kotun ta sake bayyana shi Injiniya Suleiman a matsayin zababben dan takarkar daya lashe zaben, kana ita hukumar zabe ta sake ba zababben dan majalisar takardar shaidar cin zaben bayan kotun ta tabbatar da shi.
“Don haka ba muga dalilin da zaisa shi kakakin majalisar ya ci gaba da ajiyar wanda bai dace ba kuma ya ki amincewa da shi zababben wakilin al’umma yankin saboda haka a yau muka fito don fadin abin da ke faru kuma da matakin da zamu dauka idan ba ayi abin da ya dace ba.”
“Hakazalika mun mika koken mu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Shugaban Yan Sandan Najeriya da duk wasu masu ruwa da tsaki a cikin wannan lamarin domin ganin cewa an tabbatar mana da abin muke so daga nan zuwa lokacin da muka dibar masa.”
“Muna fatan kakakin majalisar zaiyi abin da ya dace kamin lokacin wa’adin da muka dibar saboda shi ma Suleiman Aliyu matsayinsa daya yake tamkar irin na kakakin majalisar wanda duk zabensu aka yi kuma bai da ikon hana wani zababben Dan majalisar zama a zauren ba tare da wani dalili ba.”- inji Lauya Suleiman
A karshe, sun shawartar kakakin majalisar tarayyar da ya gaggauta bin umarnin kotun da amincewa ya bar zababben wakilin yankin na Jam’iyyar APC da ya koma han karagar mulkinsa.