‘Yan Kasuwar Da Suka Ci Bashinmu Sun Yi Ɓatan Dabo – Gwamnatin Tarayya

‘Yan Kasuwan da aka baiwa bashin jari karkashin shirin ‘Trader Moni’ da gwamnatin tarayya ta shirya karkashin ma’aikatar jin dadin da walwalan al’umma domin rage talauci, sun ki biya.

Jagorar shirin NSIP ta jihar Kwara, Hajiya Bashirah AbdulRazaq-Sanusi, ta bayyana hakan ranar Laraba, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Hajiya Bashirah tace kimanin mutane 10,000 suka samu bashin ‘Trader Moni’ a jihar idan aka raba musu kimanin bilyan 1.3.

Ta ce abin damuwan shine mutanen na ikirarin cewa ba zasu biya ba.

Talakawa basu shirya biyan bashin da aka basu ba saboda tunanin yan Najeriya kan duk wani abin dake da alaka da gwamnati, a ganinsu sun ci banza.

Labarai Makamanta

Leave a Reply