‘Yan Fashin Jirgin Kasan Abuja Sun Yaudari Gwamnati – Garba Shehu

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa ta ce, ‘yan ta’adan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa dake jigila daga Abuja zuwa Kaduna sun yaudari gwamnati.

Hadimin Shugaban kasa a fanin yada labarai Malam Garba Shehu, ya bayyana haka inda ya shaidawa BBC cewa gwamnatin tarayya ta biya wa shugaban wanda suka yi garkuwa da fasinjoji jirgin kasa bukatarsa amma ya saba alkawari.

Garba Shehu yace Shugaban ‘yan ta’addan ya nemi gwamnati ta saki matarsa mai juna biyu kuma bayan haka aka kai ta asibiti ta haifi tagwaye, aka nuna masa cewa matarsa da ‘ya’yansa na cikin koshin lafiya, kuma aka mika wa iyayensa su.

Malam Garba, ya kara da cewa bayan gwamnati ta yi hakan sai yan ta’addan suka kara bijiro da sabbin bukatu.

Shehu ya ce hakan bashi bane karon na farko da yan ta’adda ke saba alkawarin da aka yi da su ba, amma shi ne karon farko da gwamnatin ta faɗa da bakinta da kuma ainihin bukatun yan ta’addan.

Har yanzu akwai fasinjoji 31 a hannun masu garkuwar a cikin daji, amma gwamantin ta ce ba za ta yi amfani da karfi ba wajen ceto su, saboda dukan su su fito a raye.

Labarai Makamanta

Leave a Reply