‘Yan Boko Haram Sun Sace Mata 300 A Jihar Borno

IMG 20240229 WA0096

Raotanni daga Jihar Borno sun bayyana cewar Yan ta’addan Boko Haram, sun sace Mata da yawan su ya Kai 300 a Jihar Borno.

Wasu rahotannin na cewa, adadin matan da aka sace 113 ne, kuma mayakan na Boko Haram sun sace su a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa daji domin debo itatuwan girki a ranar Lahadin da ta gabata.

Rahotan ya ce mata sun fito ne daga daya daga cikin sansanonin Yangusun hijira dake Jihar Bornon

Kawo yanzu babu wani cikakken rahoto a hukumance dake tabbatar da adadin wadanda aka yi awon gaba da su ba, to amma kafar RfI ta ce zasu Kai 300.

Wannan dai na zuwa kwanaki kadan bayan da Gwamnatin Jihar Borno ta ce Kashi 95% cikin 100% na mayakan Boko Haram sun mutu musamman wadanda aka kafa kungiyar da su farko-farko na shekarar 2009.

Labarai Makamanta

Leave a Reply