‘Yan Bindigar Zamfara Sun Fara Kaura Zuwa Kano – Dan Majalisa

Rahotanni da muke samu yanzu na bayyana cewar hare-haren da sojoji suke kai wa ’yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara sun tilasta musu tserewa zuwa Jihar Kano da ma wasu jihohin.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Rogo da Karaye a Majaliar Wakilai, Haruna Isah Dederi, ya ce a kwanakin baya ’yan bindiga sun kai hare-hare gami da garkuwa da mutane a garuruwa bakwai a Karamar Hukumar Rogo ta Jihar Kano.

Ya ce garuruwan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane a yankin sun hada da garin Jajaye, Zarewa, Ruwan Bago, Bari, Falgore, Dutsen Ban da Hawan-Gwamna (Fulatan).

“Idan ba a gaggauta daukar matakai ba na hana yaduwar ’yan bindigar a Karamar Hukumar Rogo da wasu kananan hukumomin Jihar Kano musamman wadanda ke kan iyaka, matsalar na iya yaduwa zuwa wasu kananan hukumomi tare da gurgunta amincin da ake da shi a jihar Kano,” inji dan Honorabul Dederi.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara tsanantawa wajen ragargazar da take wa ’yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina ta hanyar fadada matakan zuwa wasu wurare.

A cewarsa, yin hakan na da muhimmanci a sauran yankunan da matsalar ta shafa domin gudanar da hare-haren a lokaci guda zai hana bata-garin samun sukunin tserewa zuwa wasu wuraren.

Related posts

Leave a Comment