‘Yan Bindigar Zamfara Ke Kisan Jama’a A Katsina – Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya koka kan ?aruwar ayyukan ‘yan bindiga a jiharsa inda kowace rana abubuwa ke ?ara dagulewa, Katsinawa na cikin tsananin tashin hankali.

Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a yayin tautaunawa da manema labarai a Kafur, inda ya bayyana cewa mafi akasarin wadannan miyagun su kan je su haddasa tashin hankali a Katsina sannan su koma mabuyarsu a Zamfara.

Gwamnan ya yi korafin cewa ‘yan bindigan na yin duk abunda za su iya don wargaza kokarinsa na dawo da zaman lafiya, tsaro da oda a Katsina.

Aminu Masari ya kuma yi kira ga rundunar sojin Najeriya da taimakon sauran hukumomin tsaro da suyi abunda za su iya domin fitar da ‘yan bindigan daga Jihar.

“Wuraren da muke da matsala kawai sune kananan hukumomin Faskari, Sabuwa da Dandume a jihar, a yankunan Jibia, Batsari, Safana da Danmusa an samu zaman lafiya.

“Daga rahotannin, da nake samu duk safe idan ka ga lamarin fashin shanu ko garkuwa da mutane to yawacinsu a kewayen Faskari, Sabuwa da Dandume ne. Muna ta kai wa hukumar soji korafi a kan su karbe ragamar yankunan Gurbi-Gidan Jaja-Kaura Namoda na jihar Zamfara.

“Har sai an dawo da cikakken tsaro a wannan yankuna, kasancewarsu masu hatsari inda yawancin ‘yan bindiga ke zama da yawo kai tsaye, idan ba haka ba, ba za mu iya kare Katsina ba ba tare da tsaro a Zamfara ba, saboda kaso 99 na dukkanin hare-hare da garkuwa da mutane da ke faruwa a Katsina daga Zamfara ne.”

Related posts

Leave a Comment