Rahotanni daga Lafiya babban birnin Jihar Nasarawa na bayyana cewar wasu gungun ‘yan Bindiga sun kaddamar da hari tare da kisan wasu manoma tara a yankin Ajimaka, wani matsugunin Tiv da ke karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 24 ga wannan wata da muke ciki, Wadanda aka kashe a Doma sune Tsekaa Chiatyo, Kwaghdoo Tsekaa, Sewiesi Tsekaa Bobo Chiatyo, Aondosee Fidelis Aboy, Igba Aduku, da Iwuesi Aseer, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.
An tattaro cewa ‘yan bindigan sun afkawa mutanen ne da misalin karfe biyu na safiyar Asabar, suna harbi ba kakkautawa a iska tare da rera wakokin ya?i.
Shugaban kungiyar Tiv Development Association (TIDA) a jihar Nasarawa, Kwamared Peter Ahemba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya yi nadamar cewa hare-haren da ake kaiwa mutanen Tiv na jihar, musamman wadanda ke zaune a yankunan kan iyaka tsakanin jihohin Benuwai da Nasarawa, sun zama abin da ake sake samu duk da kokarin da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da takwaransa na Benuwai, Dr. Samuel Ortom suka yi don tabbatar da dorewar zaman lafiya.
“A duk lokacin da makiyaya ke da lamuran da suka shafi aiwatar da dokar hana kiwo a fili da gwamnatin jihar Benuwai, sai su zo su far wa mutanenmu (Tiv) a jihar Nasarawa.” “Mu‘ yan asalin Tiv ne na jihar Nasarawa. Mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma dole ne makiyaya su daina afkawa mutanenmu kan abubuwan da ba su san komai a kansu ba.
Sai dai kuma, ya bayyana cewa mummunan lamarin ya haifar da raba dubban manoma ‘yan kabilar Tibi da muhallinsu a yankin.
Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ’yan sandan Jihar ta Nasarawa ASP Rahman Nansel, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu rahoton ba.