‘Yan Bindiga Sun Yi Sansani A Dajin Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gana da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, a ranar Laraba, 2 ga Satumba, a fadar shugaban kasa kan matsalar tsaro a jihar.

Yayin da yake jawabi bayan ganawar, ya ce ya bayyanawa mataimakin shugaban kasa kokarin da sukeyi wajen magannce matsalar tsaro a jihar. Ya ce jami’an Soji tare da sauran hukumomin tsaro na iyakan kokarinsu wajen dakile ‘yan bindigan da suka shiga dajin Falgore.

Ya ce jihar na fuskantar kalubale daga dajin Falgore saboda Sojoji na fuskantar matsala wajen dakatar da ‘yan bindiga, musamman ‘yan ta’adda wajen mamaye don kai hare-hare.

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin Arewan da basu fuskantar matsalar tsaro da hare-haren ‘yan bindiga duk da cewa ta nada iyaka da jihar Katsina da Kaduna dake fuskantar matsalar tsaro.

Amma, wasu kauyukan jihar sun fara fuskantar matsalar garkuwa da mutane ‘yan kwanakin nan. A kauyen Kore dake karamar Dambatta misali, an yi garkuwa da diyar wani dan majalisa, Juwairiyya Kore, a ranar 22 ga Yuli, 2020.

Masu garkuwa da mutane sun zo sace uban ne amma da basu sameshi ba, sai sukayi awon gaba da diyar. An saketa bayan kudin fansan da aka biya. Yarinyar ta ce an kaita wani gida dake cike da ‘yan Bindiga.

Dajin Falgore na kewaye da kananan hukumomin Tudun Wada, Doguwa da Sumaila a jihar Kano. Hakazalika dajin na iyaka da jihar Bauchi da jihar Kaduna.

A Yulin 2020, kwamishanan ‘yan sandan jihar Kano, Habu Sani, ya bayyanawa jami’an yan sanda musamman wadanda ke hanyar Kano-Kaduna da Kano-Jos, su shirya saboda akwai yiwuwan hari daga ‘yan bindiga.

Wata daya bayan jawabin da yayi, ‘yan bindiga sun kai wa matafiya hari a watan Agusta. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigan masu dauke da manyan makamai, suka tare hanyar na tsawon awanni kuma suka sace mutane uku.

Daga cikin wadanda aka sace akwai kwamandan Hisbah na karamar hukumar Doguwa, Mallam Mukhtar Abdulmumin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply