Rahotanni daga Jihar Binuwai na cewa wasu ‘yan bindiga ?auke da manyan makamai sun sace daliban Jami’ar nazarin aikin noma ta tarayya ta makurdi (FUAM) a jihar Benue da ke arewacin kasar.
Hukumomin makarantar sun tabbatar da faruwar lamarin, suna cewa har yanzu ba a san adadin daliban da aka sace ba a daren ranar Lahadi.
Daraktar yada labarai da hulda da jama’a Mrs Rosemary Waku ce ta bayyana bayyana faruwar lamarin a ranar Litinin.
Lamarin sace sacen daliban manyan makarantu na neman zama ruwan dare yanzu a tarayyar Najeriya musamman yankin Arewacin kasar.
A makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka sace daliban wata jami’a mai zaman kanta a Kaduna, sannan daga bisani suka harbe uku daga cikin su.