Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa a yayin da ake cika kwanaki bakwai da ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya a garin Gidan Dan Zara na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, maharan sun bukaci ragowar jama’ar garin su biya kudin fansar mutanen da ake garkuwa da su, kuma su biya wa garin harajin zama lafiya.
‘Yan bindigan da suka kai hari garin Gidan Dan-Zara na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara a makon da ya gabata, inda suka kona gidaje da masallatai da sauran kadarori, kuma suka sace mutum 64, a yanzu sun kara jefa garin da ’yan ragowar jama’arsa cikin wani sabon tashin hankali kamar yadda wani mazaunin garin ya yi karin haske:
”Mutanen nan su na can hannun wa’dannan muane kuma sun bukaci ku’da’den fansa, wanda in ba a bayar ba su na ikirarin za su kashe su, shi kan shi garin kuma sun bukaci cewa akwai kudi da za a biya na sasanci kan garin, kamar shi ma ya zama kudin fansa kenan su na barazanar tashin garin gaba daya”.
Dangane da wannan batu BBC ta tuntuɓi Sulaiman Bala Idris, mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, da ASP Yazid Abubakar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar.
Sai dai a wani abu mai tangan da arashi, dukkansu sun yi alkawarin bincikawa, kuma su sake kiran mu, amma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ba mu ji daga gare su ba.
Sharuddan da ‘yan bindigan suka gindaya dai, suna zuwa ne yayin da mutane garin na Gidan Dan-Zara suke kokowar gyara ta’adin da maharan suka tafka a makon da ya gabata. Ga kuma abin da mutumin garin ke cewa:
”Ana nan dai ana gyare-gyaren ta’adin da aka samu da kuma asarar gidaje da rumbuna, amma masallatai da gidaje ba za a iya gyaru ba a yanzu, masallatai wurare ne na Ibada tilas sai hankalin jama’a ya kwanta sannan za suyi maganar gyara, Sallar ma a waje ake yin ta. Idan ba a biya wadannan kudade ba su na barazanar cewar”.
Yanzu dai kallo ya koma ne ga batun yadda hukumomin da abin ya shafa asu fuskanci wannan wala-gigi da ‘yan bindiga ke ci gaba da yi da jama’ar yankuna da ‘kauyuka da dama ba wai a jihar Zamfara ka’dai ba har ma da har ma a sauran jihohin da ke fama da irin wannan matsala ta tsaro a Najeriya.