‘Yan Bindiga Sun Taso Jihar Kaduna Gaba

IMG 20240310 WA0186

Rahotanni na daga jihar Kaduna na cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutum fiye da 80 a garin Kajuru a wani sabon hari da suka kai garin ranar Lahadi.

Harwayau, ‘yan bindigar sun fasa shaguna inda suka saci kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki kamar yadda wani shaida ya fada wa BBC.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansur Hassan ya tabbatar da sace mutanen ga BBC sai dai bai fadi yawan adadin da kafafen watsa labarai ke ambatawa ba.

Hassan ya ce nan ba da jimawa ba za su sanarwa da manema labarai da jama’a iya adadin mutanen da aka sace kasancewar har yanzu ana tantancewa.

“Eh, gaskiya mun samu wannan labari na masu garkuwa da mutane sun sake sace mutane da dama, amma har yanzu ba a san iya adadin mutanen da aka sace ba saboda daji ne gurin.” in ji Hassan

“Shiyasa kullum muke kira ga jama’a da cewa duk lokacin da suka ga gittawar waɗannan mutanen, ba sai laile sun kai hari ba, a yi ƙoƙari a sanar da mu saboda irin waɗannen wurare daji ne sosai”

“Saboda kusan yaƙin da ake yi da waɗannan ƴan ta’adda da kusan jama’an gari ake yi.

Hassan ya ce rundunar jihar ta tura ƙarin jami’an tsaro don bin sawun mutanen da aka ƙara sacewa.

Harin dai na zuwa ne ƙasa da kwana biyu bayan an sace wasu mata fiya mata 15 tare da wani namiji ɗaya a ƙauyen Dogon Nama duk dai a ƙaramar hukumar ta Kajuru.

Labarai Makamanta

Leave a Reply