Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

‘Yan Bindiga Sun Sake Sabunta Hari A Jihar Kaduna

Rahotanni dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun sake kashe mutane a wasu kauyuka biyar tare da yin garkuwa da wasu 16 a kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Giwa dake jihar.

Wannan lamari ya faru ne da safiyar ranar Lahadi lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyen, inda suka shiga harbi na kan mai uwa da wabi.

Wani tsohon kansilan yankin, Daiyabu Kerawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mazauna kauyen sun fice dag kauyen bayan harin na ‘yan Bindiga.

Babu wani martani a hukumance daga gwamnatin jihar amma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, ya yi alkawarin samar da cikakken bayani kan lamarin.

Wasu bayanai guda biyu da kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya bayar a ranar Lahadin da ta gabata sun tabbatar da kisan da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi.

Ya ce jami’an tsaro sun kai wa gwamnatin jihar Kaduna rahoton cewa mutane hudu sun mutu, daya kuma ya jikkata, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a Kerawa, karamar hukumar Igabi.

“A cewar rahoton, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen, inda suka yi ta harbe-harbe, sannan suka kashe mazauna garin hudu, Lado Shuaibu, Usman Haruna, Ayuba Muntari da Jafar Abdullahi.

“An bar Mallam Mamuda da rauni, yayin da ‘yan bindigar suka kwashe wasu babura da kayayyaki daga al’umma.” An samu munanan hare-hare daban-daban a jihar a cikin ‘yan kwanakin nan.

Exit mobile version