Wasu da ake zargin ?an bindiga ne sun sace wasu matasa ?an Kasuwar Kantin Kwari ta Kano a kan hanyarsu ta zuwa birnin Aba na jihar Abia da ke kudancin Najeriya.
?an bindigar sun tare matasan wa?anda dukkansu ?an jihar Kano ne, a kan hanyarsu ta zuwa Aba a cikin daren ranar Lahadi.
A cewar ?ungiyar matasan arewacin Najeriya a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, matasan sun tafi garin na Aba a ranar Lahadin da ta gabata don yin sayayya, da niyyar koma wa Kano a makon da muke ciki.
Sai dai ?ungiyar ta ce suna cikin tafiya sai wasu ?an bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne don neman kudin fansa suka harbi tayar motar safa da suke ciki, suka kuma yi awon gaba da su da sauran fasinjojin da ke cikin motar sama da 50.
Sannan kungiyar ta ce ba su sami labarin halin da abokan nasu ke ciki ba sai a ranar Laraba, inda masu garkuwar suka nemi ku?i kafin su bayar da matasan.
Da farko rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, amma kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Kaduna ya fitar da sanarwa inda ya ce a kan hanyar Kaduna lamarin ya faru ba.
“Hukumomin tsaro na tarayya da ke aiki a kan titin Kaduna-Abuja a wannan lokacin ba su bayar da rahoton faruwar wani lamari kamar haka ba.
“Sannan dukkan binciken da jihar Kaduna ta yi bai gano cewa lamarin ya faru ba a fa?in jihar,” a cewar sanarwar.Shugaban ?ungiyar matasan ?an kasuwar Arewacin Najeriya da ke Kasuwa Kwari a Kano, Abubakar Babawo ya ce “Sun tafi Aba ne don saro takalma da yaduka amma sai wannan mummunan abu ya faru da su. A?alla sun kai 27 kuma yawancinsu masu ?aramin ?arfi ne don ku?a?ensu ba sa wuce naira 300,000.
“Suna ?an zuwa sare-sarensu ne don samun abin rufin asiri. A cikinsu akwai wanda ba a da?e da yaye shi ba aka ba shi ?an jarin da zai dogara da kansa amma sai ga abin da ya faru.”
Ya ?ara da cewa mutanen sun tuntu?i dangin ?an kasuwar ana ta ciniki. “Amma tuni mun tuntu?i jami’an tsaro,” in ji Abubakar.
Sai dai ba wai iya wadannan yan kasuwar ‘yan bindigar suka ?auke ba, har da sauran sama da mutum 50 da ke cikin motar safa da ke safara tsakain arewaci da kudancin Najeriya da ke iya ?aukar kusan mutum 100.
Sai dai BBC ta yi kokarin jin ta bakin wasu daga cikin makusantan wa?annan matasa da ake zargi ?an bindiga sun sace, sai dai ha?a ba ta cimma ruwa ba, sakamakon ?in magana da suka yi, sannan wasu daga cikinsu ma ba su san an ?auke yaransu ba.
Wannan dai na zuwa ne makwanni kadan bayan da wasu ?an bindiga suka dauke wani dan kasuwa a garin Minjibir, sannan suka ?ona motar ?an sanda, amma sai dai bayan biyan kudin fansa sun sako mutumin.
A baya-bayan nan al’ummar Najeriya musamman direbobi da ke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja na kokawa kan yadda masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa suka ddabi hanyar.
Sai dai duk da ikirarin da hukumomin Najeriya ke yi na shawo kan al’amarin, abin na ci gaba da jefa tsoro da faragaba a zukatan al’umma.