‘Yan Bindiga Sun Sace ?alibai Da Dama A Jami’ar Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ?auke manyan makamai sun kai hari kan Jami’ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka sace dalibai da dama.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun kai hari a Jami’ar ne da daren Talata inda suka yi awon gaba da dalibai da yawa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kaduna Mohammed Jalige, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kara da cewa “ya zuwa yanzu ba mu kai ga tantance adadin daliban da aka sace ba.”

A cewarsa “yanzu muna wurin da lamarin ya faru, don haka sai mun samu rijistar makarantar sannan za mu san yawan daliban da aka sace.”

An sace daliban ne daga dakunansu kuma rahotanni sun ce daliban maza da mata ne.

Jami’ar Greenfield ta ‘ya’yan masu hannu da shuni ce wadda aka bude a shekarar 2019.

A watan jiya ne ‘yan bindiga suka sace ?alibai 30 daga Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Abubuwan da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation a unguwar Mando a cikin garin Kaduna.

Kodayake an kubutar da dama daga cikinsu, amma har yanzu wasu daliban suna hannun mutanen da suka yi garkuwa da su.

Jihar Kaduna na cikin jihohin da suke fama da hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman fansa.

Gwamnatin jihar Kaduna ta sha bayyana cewa ba za ta yi sulhu da ‘yan bindiga ba domin kuwa suna kashe mutane ne babu gaira babu dalili.

A wata hira da BBC Hausa kwanakin baya, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce ya kamata a bu?e wa ‘yan bindigar wuta har sai an ci karfinsu.

Related posts

Leave a Comment