‘Yan Bindiga Sun Nemi Miliyoyin Kuɗi Kafin Sakin Marayun Abuja

‘Yan bindigar da suka sace wasu marayu daga gidan da ake kula da su a babban birnin tarayya Abuja sun bukaci a biyan diyyar naira miliyan 10 akan kowanne maraya guda kafin sakinsa.

‘Yan bindigar sun kuma bukaci biyan naira miliyan goma kan mai gadin gidan da wani magidanci Momoh Jimoh da iyalinsa, da kuma wata mata Rukaiyat Salihu.

Wata majiya a gidan marayun ta shaidawa Jaridar Daily Trust cewar, ‘yan bindigar sun buga waya a ranakun Lahadi da jiya Litinin domin neman diyyar.

Wani dan uwan magidancin da aka sace ya tabbatar da bukatar biyan diyyar, sai dai rundunar ‘yan sandan Abuja bata ce komai ba dangane da bukatar.

Sace Marayun da ‘yan bindigan suka yi a Abuja ya zama wani lamari mai tayar da hankali tun bayan sace ɗaliban makarantar Sakandare ta ƙaramar Hukumar Ƙanƙara Jihar Katsina a kwanakin baya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply