Wani rahoto da ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna ta fitar ya nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na 2021 an kashe mutum 323 tare da yin garkuwa da mutum 949 a jihar.
Samuel Aruwan, Kwamishinan da ke kula da ma’aikatar ya bayyana cewa al?aluman na nuna mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ayyukan ?an bindiga da fashin daji da garkuwa da mutane da hare-haren ramuwa, ciki har da mahara da ?an bindigar da jami’an tsaro suka kashe.
Sai dai ya ce bai ha?a da jami’an tsaro da suka mutu a bakin aiki ba.
Haka kuma, al?aluman ba su ha?a da mutanen da suka rasu sanadiyyar ha?urran abubuwan hawa da kisan kai ba.
Mutanen da suka rasu
Rahoton ya nuna cewa cikin mutum 323 da suka rasu, 20 mata ne yayin da 11 daga cikinsu ?ananan yara ne da shekarunsu ba su kai 18 ba.
Haka kuma mutane 236 daga ciki sun fito ne daga yankin Kaduna ta Tsakiya – wato a ?ananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Igabi da Chikun da Kajuru, sai duk cikinsu Birnin Gwari ke da mafi yawan mutanen da suka mutu, mutum 77.
Yankin Kaduna ta Kudu na da mutum 68 da suka rasa rayukansu kamar yadda rahoton ya bayyana yayin da Kaduna ta Arewa ke da mutum 19.
Mutanen da aka yi garkuwa da su
Rahoton ya bayyana cewa cikin mutum 949 da aka yi garkuwa da su, yankin Kaduna ta Tsakiya ne ya fi yawan mutanen inda aka yi awon gaba da mutum 782 a ?ananan hukumomin Birnin Gwari mai mutum 291 haka kuma Igabi na da mutum 227.
Sauran ?ananan hukumomi da aka fi garkuwa da mutane a jihar sun ha?a da Chikun (mutum 156) da Giwa (mutum 58) da Kajuru (mutum 46) duk a yankin Kaduna ta Tsakiya.
A yankin Kaduna ta Kudu an yi garkuwa da mutum 129 a cewar rahoton yayin da aka yi garkuwa da mutum 38 a yankin Kaduna ta Arewa.
Gaba ?aya an yi garkuwa da maza 550 da mata 317 da ?ananan yara 82 a jihar a watanni ukun farko na wannan shekara.
Mutanen da suka samu raunuka
A ?angaren mutanen da suka samu raunuka dalilin hare-haren da ayyukan ?an bindiga da rikicin ?angare a jihar, rahoton ya nuna cewa mutum 244 suka samu raunuka.
Daga cikinsu kuma 25 mata yayin da 6 ?ananan yara ne da shekarunsu ba su haura 18 ba.
A wani ?angare na rahoton, an gano cewa an sace shanu 3,289 a fa?in jihar.
Me gwamnati ke yi game da batun tsaro a jihar a wannan shekarar?
Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta samar da hanyoyi da take ganin za su fi dacewa wajen shawo kan ?alubalen tsaro da ta ke fuskanta.
Ya ce gwamnati na ?arfafa ayyukan le?en asiri na cikin gida musamman a yankunan da matsalar tsaro ta fi ?amari.
Haka kuma, tana taimakawa jami’an tsaron gwamnatin tarayya tare da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar.
Rahoton Mista Aruwan ya bayyana cewa jihar Kaduna ta hanyar hukumar samar da zaman lafiya ta Kaduna State Peace Commission na tattaunawa da al’ummomi kan hanyoyin warware matsaloli cikin kwanciyar hankali mai makon ta hanyar daukar fansa.
Sannan ya ce akwai tsare-tsare da gwamnati ta samar musamman a yankunan da rashin tsaro ya fi tsauri kamar Birnin Gwari da Giwa da Igabi da Zaria inda ake zaton ?an bindiga da masu garkuwa da mutane na ?uya.
Rahoton ya bayyana cewa akwai jami’an tsaro na musamman da aka tura Dajin Falgore da ke kan iyakar jihar Kaduna da jihar Kano wanda kuma ya yi ?aurin suna a matsayin matattarar masu aikata manyan laifuka.
Rahoton ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa watan Maris kawai, an yi amfani da na’urori wajen ?aukar bayanan jihar daga sama a ?alla sau 150 don gano wuraren da ?an bindiga suka fi aiki.
An kuma kai hare-hare ta sama a wuraren da aka gano su a Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Kachia da ma wasu ?angarorin jihar Neja mai ma?wabtaka.
Mista Aruwan, a cikin rahoton nasa ya ce kawo yanzu an kashe ?an bindiga 64 a jihar.