‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Sarkin ?auran Namoda Hari

Wasu miyagu da ake zargin yan bindiga ne sun tare tawagar Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kauran Namoda a Jihar Zamfara inda suka kashe mutum takwas ciki har da yan sanda guda uku.

Lamarin ya faru ne a babban titin Gusau zuwa Funtua yayin da basaraken ke kan hanyarsa ta zuwa wani taro a gusau yayin da yan bindigan suka afka wa tawagarsa suka kashe yan sanda guda uku.

An kuma kashe wani direban Hilux a tawagar, da babban dogarin sarki da wani Dan Amal, wadda kawu ne ga sarkin na Kauran Namoda.

Mun yi kokarin kiran kakakin rundunar yan sandan jihar domin jin ta bakin sa amma bai daga wayar ba kuma bai kira ba. Zamfara, kamar sauran wasu jihohin Arewa na fuskantar kallubalen tsaro inda yan bindiga da masu garkuwa ke kai wa mutane hari akai akai. Ko baya bayan nan ma wasu yan bindigan sun sace dalibai daga makarantar kwana ta Kankara a Jihar Katsina. Sai dai bayan yan kwanaki gwamnati da hadin gwiwar gwamnan zamfara da sauran jami’an tsaro suka ceto yaran.

Related posts

Leave a Comment