‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Sabon Hari A Abuja

IMG 20240227 WA0004

‘Yan bindiga sun kai sabon farmaki gundumar Kawu da ke karamar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis. A yayin harin, sun yi awon gaba da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na gundumar, Alhaji Alhassan Sidi Kawu da ƴayansa hudu da wasu mutane 18.

Shugaban karamar hukumar Bwari, Abdulmumini Zakari, ya shaidawa manema labarai cewa ƴan bindigar sun dira gundumar ne a ranar Laraba daga dajin Kuyeri da ke Kaduna.

Ya kara da cewa akwai mata da yaron mai gundumar yankin, Alhaji Abdulrahman Danjuma Ali a cikin wadanda aka sace, rahoton The Punch. Yadda ƴan bindigar suka kai farmakin Zakari ya ce: “Sun raba kansu ne gida gida, wasu suka tafi gidan mai sarautar gudnumar, Alhaji Abdulrahman, inda suka sace amaryarsa da yaronsa Lukman.

“Wasu kuma sun farmaki gidan Alhaji Alhassan Sidi Kawu, Marafan Kawu kuma tsohon shugaban PDP na gundumar, sun tafi da shi da yaransa hudu.” Yan sanda ba su ce uffan kan harin ba Haka kuma an ruwaito cewa ƴan bindigar sun farmaki gidan Sarkin Pawan Kawu, Gambo Pawa, wanda suka sace shi tare da matansa biyu da yara.

Duk wani yunkuri na manema @ na jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ya ci tura.

Labarai Makamanta

Leave a Reply