Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ofishin ‘yan sanda na Arum Inyi da ke karamar hukumar Oji-River a jihar Enugu tare da kashe mutum biyu sannan suka cinna wa ofishin wuta.
Gidan Talbijin na Channels TV ya ruwaito cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da makamai da harsasai a harin da suka kai da safiyar ranar Lahadi.
Yayin kai harin an jiyo ‘yan bindigar na rera wakokin adawa da yin zabe inda suke cewa ”babu zabe, babu ‘yan sanda a kasar Biafra”.
A bidiyon da yada an ga ginin ofishin na ci da wuta, tare da gawar mutum biyu kwance a gefen katangar ginin.
Inda wasu muryoyi da ake iya ji a cikin bidiyon ke cewa gawarwakin mutanen biyu ‘yan sanda ne.