‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Ƙato Da Gora A Kaduna

Rahotanni daga Kaduna sun bayyana cewar wasu Jami’an sintirin jihar waɗanda aka fi sani da ‘yan ƙato da gora sun gamu da ajalinsu yayin wata arangama da ‘yan bindiga a karamar hukumar Chikun, da yammacin Talata.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka ranar Laraba a wata takardar sanarwa da ya fitar.

Ya kuma ce daga baya sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan Bindigar da suka kaiwa jami’an hari, a kauyen Dande a babban garin Bukuru dake yankin ƙaramar Hukumar Chikum.
“Jami’an sun kuma lalata maboyar yan tawayen dake yankin,” a cewar sa.

Kwamishinan ya bayyana sunayen jami’an a matsayin Alison Musa, Dauda Audu da Ishaya Sarki. Ya ce ragowar mutum biyu, Ayuba Tanko da Doza Adamu sun ji rauni.

Mr Aruwan ya kuma ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya mika ta’aziyya ga iyalan wanda abin ya shafa.
“Gwamnan ya yabawa sojojin sama dana kasa na “Operation Thunder Strike” a wani atisaye da suka sami nasara a yakin Kuku, a karamar hukumar Kagarko a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply