An shiga matsananciyar firgita a yankin Kudancin Jihar Kaduna biyo bayan wani harin sanyin safiya da wasu ‘yan Bindiga ?auke da manyan makamai suka kai a kauyen Ungwan Bido da ke karamar hukumar Jema’a.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, su suka kaddamar da harin da sanyin safiyar ranar Lahadi suka karkashe mutane da dama.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, wanda ya tabbatar da lamarin ya kuma bayyana cewa harin ya biyo bayan rahoton kisan wani Isiyaka Saidu.
An kashe Saidu wanda ya kasance makiyayi a kauyen Ungwan Pah a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba. A halin da ake ciki, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi martani kan sabon harin sannan yayi Allah-wadai da lamarin.
Yayinda yake jaje ga iyalan mamatan da wadanda aka raunata, gwamnan ya umurci hukumomin tsaro da su yi bincike da kamo dukkanin masu hannu a ta’asar.
An tabbatar da cewar Maharan sun kashe mutane 7 tare da ?one gidaje da dukiyoyi da dama.