Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewar ‘yan bindiga sun tafka mummunan ta’asa na kisan jama’a bayin Allah wadanda ba su jiba kuma basu gani ba, Hukumar yan sanda a jihar Kebbi a ranar Asabar ta tabbatar da kisan mutum 88 da tsagerun yan bindiga suka yi a karamar hukumar Danko/Wasugu na jihar Kebbi.
Kakakin hukumar, Nafi’u Abubakar ya bayyana cewa wannan ya auku ne duk a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ?asa NAN ya ruwaito.
Yace an kashe su ne a hare-haren da aka kai garuruwa takwas a karamar hukumar. A cewarsa, kawo yanzu an gano gawawwakin mutum 88 kuma an tura jami’ai tabbatar da tsaro a yankin.
“An kashesu ne a garuruwan Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da Iaguenge, duka a karamar hukumar Danko/Wasugu na jihar Kebbi,” Abubakar yace. “Da farko, gawawwaki 66 aka gano amma yanzu haka, an gano gawawwaki 88.”