Babban Malamin Addinin Musulunci nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, ya bayyana cewar a fili yake ganin ‘Yan Bindiga ya fi sauki akan ganin Shugaban Kasa Buhari babu shakka a hakan.
A cewar Sakataren Ƙungiyar Dattawan Arewa Dr Hakeem Baba Ahmed, yace Dr. Ahmad Gumi ya faɗawa masu ruwa da tsaki a yankin cewa ya daɗe yana ƙoƙarin ganin Buhari kan batun tabarɓarewar tsaro amma hakan bai yi wu ba.
Malamin addinin ya ziyarce dazuka daban-daban domin tattaunawa da ƴan bindigan da nufin kawo karshen hare-haren da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.
“Yau, Sheikh Dr Abubakar Gumi ya shaidawa mutanen wurin taro a Kaduna yadda ya shafe watanni yana ganawa da yan bindiga, da kuma karin wasu watannin yana ƙoƙarin ganawa da shugaban kasa domin ya bashi shawara kan yadda za a magance matsalar amma abin ya gagara.
Ya ce ganin ‘yan bindiga ya fi ganin shugaban ƙasa sauƙin,” kamar yadda Baba Ahmed ya wallafa a Twitter. Rubutun da Baba Ahmed ya wallafa a Twitter ya janyo cece-kuce amma kakakin na kungiyar arewa ya kare abin da ya rubuta.
“An riga an san matsayar Gumi a kan ƴan bindiga. Dole ne sai ya gana da shugaban kasa gaba-da-gaba kafin ya bashi shawara.”
Baba Ahmed ya bada amsa kamar haka, “Ta yaya zan yi jayayya da wanda ya fi ni sanin harkokin tsaro ko yadda za a magance su? Abin da na sani shine Gumi tsohon Kanar ne a rundunar soja kuma akwai yiwuwar ya gano wasu abubuwa da za su yi amfani idan ya faɗa wa shugaban kasa gaba-da-gaba. Mai na sani?”
Mustapha Hadi ya yi tambaya, “Shin Gumi bai zai iya bawa Ministan tsaro shawararin ba?” Baba Ahmed ya mayar da martani, “Ministan tsaro yana karkashin shugaban kasa ne, don haka shugaban kasa ne ke ɗaukan matakin karshe kan batutuwan tsaro.”