Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa hare-haren ‘yan bindiga ya yi sanadiyyar raba mutum 289,375 daga gidajen su, a cikin yankuna 551 a ƙananan hukumomi 12 na cikin jihar.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Usman Mazadu ne ya shaida haka, yayin da ake raba kayan abincin tallafi ta marasa galihu a garin Maraban Kajuru, a ranar Laraba.
Mazadu ya bayar da dalla-dallar wasu wuraren da matsalar ta fi shafa, kamar Chikun inda ya ke mutum 26,345 sun rasa muhallin su, a cikin kauyuka 134 sai kuma Birnin Gwari inda mutum 70,893 suka rasa muhalin su a ƙauyuka 84.
Duk da haka, Sakataren Hukumar ta KADSEMA ya ce gwamnati ta jajirce wajen ƙoƙarin bayar da tallafin gaggawa da waɗanda wannan bala’i ya shafa.
Mazadu ya gode wa Gwamna Uba Sani, saboda ware Naira biliyan 11.4 domin raba kayan tallafi ga waɗanda ibtila’in ‘yan bindiga ya shafa.
Ya ce za a raba kayan tallafin ga waɗanda hare-haren ya shafa nan da makonni kaɗan masu zuwa.