Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar wasu gungun ‘yan bindiga sun farmaki wani kamfanin gona a garin Anchau na karamar hukumar Kubau dake jihar inda suka yi mummunan ta’adi.
Rahotanni sun bayyana cewar tsagerun ‘yan Bindigar sun bindige wani soja har lahira tare da yin awon gaba da wasu jami’an kamfanin gonar mutum biyu da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba.
An tattaro cewa, daya daga cikin wadanda aka sacen wani dan kasar Zimbabwe ne da ke aiki a kamfanin. Wani dan banga da ke aiki a unguwar da abin ya faru ya ce sunan dan kasar Zimbabwe din da aka sace Mista Charles Choko.
A cewarsa: “Sun kashe wani soja da ke aiki a kamfanin na gona tare da yin awon gaba da wani mutumi mai suna Charles Choko dan kasar Zimbabwe da wani Yusuf Aliyu Bello dan jihar Kano.”
Wani mutumin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa, ya ga tawagar jami’an tsaro a ranar Juma’a tana shiga dajin da ke yankin domin nemo wadanda aka sacen. An kira shugaban karamar kukumar, Basher Suleiman Zuntu, amma ba a same shi ta waya ba. Haka nan, bai mayar da sakon tes da aka tura masa ba.