‘Yan Bindiga Sun Bindige Babban Limamin Kirista A Kaduna

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar An kashe Rev. Silas Yakubu Ali na Cocin ECWA, dake gari Kibori-Asha Wuce a karamar hukumar Zango-Kataf na jihar Kaduna.

Marigayin ya tafi Kafanchan ranar Asabar din da ta gabata, amma ba a gan shi ba, har sai da wani kwamitin bincike ya gano gawarsa a yankin Kibori, kusa da garin Asha-Awuce, da safiyar jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da lamarin ga manema labarai, Kwamishinan Tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce, jami’an tsaro na kan bin sawun maharan da sukayi kisan gillan.

“Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya nuna matukar bacin rai kan rahoton kisan, wanda ya bayyana a matsayin abin tsoro da rashin tausayi. Gwamnan ya yi addu’ar fatan Alheri ga mamacin ”in ji kwamishinan.ADVERTISEMENT

Kazalika ya ce, “ Gwamna El-Rufai ya aika da ta’aziyarsa ga iyalan Rabaran Silas Yakubu Ali, da kuma Cocin ECWA da ke garin Kibori-Asha Awuce, yayin da yake addu’ar Allah ya ba su karfin gwiwa da zuriyar wannan rashi mai radadi.”

A karshe Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, “Gwamnan jihar ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kamo wadanda suka aikata wannan mummunan kisan, yayin da ya yi kira ga mazauna yankin, da su kwantar da hankalinsu. Hukumomin tsaro na gudanar da bincike a yankin baki daya.”

Related posts

Leave a Comment